16 Yuli 2020 - 13:58
Assad Ya Jaddada Cikakken Goyon Bayansa Ga Al'ummar Falastinu

Shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad ya bayyana goyon bayansa ga al-ummar Falasdinu kan gwagwarmayan da take yi da HKI don dawo da kasarsu daga ta mamaye.

ABNA24: Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya nakalto shugaban yana fadar haka a wata wasikar da ya rubutawa shugaban Falasdinawa Mahmood Abbas. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Siriya ba zata yi kasa a guiwa ba, wajen tallafawa al-ummar Falasdinu a dukkan bangarorin da suke gwagwarmaya da yahudawan Isra’ila.

Shugaba Asad ya ce yana tare da Falasdinawa a kan yin watsi da yarjejeniyar karni da kuma allawadai da kokarin mamayar yankin gabar yamma da kogin Jordan.

Kafin haka dai shugaban al-ummar Falasdinu Mahmood Abbas ya rubutawa shugaban kasar ta Siriya wasika inda yake nuna debe kaunarsa daga shuwagabannin kasashen larabawa na yankin tekun farisa. Ya kuma fadawa shugaba Asad irin halin da al-ummar Falasdinu take ciki a halin yanzu.

342/